Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Yayi Tur da Trump Dan Takarar Republican


Shugaba Obama a Laos
Shugaba Obama a Laos

Tun daga kasar Laos dake gabashin Asiya inda yake taro shugaban Amurka yayi allawadai da Donald Trump dan takarar jam'iyyar Republican

Shugaba Obama yace Donald Trump wanda yake neman shugabancin kasar bai cancanta ya zamo babban kwamandan koli na dakarun kasar Amurka ba.

Obama ya fadi haka ne a matsayin mayar da martani bisa ga kalamun Donald Trump wanda yace shugaban Rasha Vladimir Putin ya fi Obama zama shugaban kwarai.

Shugaban na Amurka yace bana tsammanin Trump ya cancanta ya zama shugaban kasa kuma kodayaushe ya bude bakinsa yayi magana yana kara tabbatar da hakan.

Da maraicen ranar Laraba ne Trump ya fada a kafar talibijan da aka kalla a duk fadin kasar yace Putin ya fi Obama zama shugaban gasken gaske kana ya kara da cewa Obama ya mayar da janarorin kasar tamkar banza.

Shugaba Obama wanda yake yankin Asiya yayinda wa'adinsa ke kusan karewa yace 'dole a matsayinka na shugaba ka san abun da kake fada, ka tabbatar da sahihancin kalamunka, kana kuma duk abun da zaka fada ka tabbatar zaka iya aiwatar dashi".

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG