Masaukin bakin gasar, Ivory Coast ce ta ci Najeriya a wasan karshe na gasar.
Ku Duba Wannan Ma Ivory Coast Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Bayan Ta Ci Najeriya 2-1 Ku Duba Wannan Ma Shugaban Kasa Tinubu Ya Karrama ‘Yan Wasan Super Eagles Da Lambar Girmamawa Ta Kasa Ta (MON)An ruwaito cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta NFF na tattaunawa kan sabunta kwantiragin kocin da ta kawo karshe a watan Fabrairun da ta gabata.
Peseiro ya ce "a jiya muka kawo ƙarshen kwantiragin da ke tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Najeriya NFF.
"Abin farin ciki da alfahari ne koyar da tawagar Super Eagles. Watanni 22 kenan da muka kwashe muna wannan sadaukarwa da matukar sha'awar aikin. Muna jin mun yi abin da ya kamata," kamar yadda kocin ya wallafa a shafinsa na X.
Peseiro ya nuna godiya ga shugabanin hukumar NFF na baya-bayanan da mai ci wato Amaju Pinnick da Ibrahim Gusau, Babban Sakataren Hukumar, Mohammed Sanusi da Sakatare Dayo Enebi.
Ya kuma nuna godiyarsa ga ‘yan wasa da ma’aikatan tawagar da suka mara masa baya a watani 22 da ya horar da 'yan wasan tawagar.