Kocin Chelsea Maurizio Ya Sassauta Tsauraran Ka'idojin Cin Abinci

Baya da kugiyar kwallon kafa ta Real Madrid tasha kashi a hanun takwarata Atletico Madrid a wasan karshe na cin kofin Super Cup na yankin turai daci 4-2 a ranar Laraba 15/8/2018.

Kungiyar ta Real Madrid ta nuna sha'awarta na ganin ta dauko danwasa maitsaron baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, maisuna Marcos Alonso, dan shekara 27, da haihuwa.

Danwasan tsakiya na Manchester United wadda ya taimaka wa kasarsa ta faransa ta lashe kofin duniya 2018 Paul Pgoba, yana da bukatar barin kungiyar domin hadewa da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, koda zasu samu rashin jituwa da Kocin kungiyar Jose Mourinho.

Shikuwa a nasa bangaren Mourinho ya shaida wa Paul Pgoba daya furta da bakinsa cewar yana son zai bar kungiyar. Inda shi kuwa danwasan mai shekaru 25 da haihuwa yace shi zaiyi magana da Mourinho kawai ta tsakaninsa da wikilinsa.

Tsohon kocin kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane yana son ya koma aikin koyarwa amman kuma yana shaawar jan ragamar Manchester United a lokacin bazara mai zuwa.

Daraktan kulob din Barcelona Ariedo Braida ya ce kungiyarsa ba zata nemi dan wasan Manchester United Paul Pogba, a wannan lokacin bazarar ba, amma ya bayyana cewa dan kasar faransar mai shekara 25 a dunita a matsayin fitaccen dan wasa, kuma ya ce kulob din zai cigaba da bibiyansa.

Kungiyar Schalke tana sha'awar sayen wasu 'yan wasa kan yarjejeniyar din-din-din, amma ba ta bukatar sayen dan wasan bayan Tottenham dan Ingila Danny Rose, mai shekara 28 ko kuma dan wasan tsakiyar Chelsea dan Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 22, akan yarjejeniyar aro.

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa na Chelsea Maurizio Sarri ya sassauta tsauraran ka'idojin cin abinci kafin wasa, da tsohon kocin kulob dun Antonio Conte ya kafa a baya.

Sarri ya yi wa dan wasan tsakiyar kungiyar ta Chelsea, Danny Drinkwater, murna domin za a sayar da dan wasan mai shekara 28 a wannan watan, kafin rufe hada hadar saye da sayarwa na bana.

Lionel Messi ba zai sake bugawa Argentina ba a wannan shekarar, kuma babu tabbacin ko dan wasan gaban na Barcelona mai shekara 31 zai sake koma taka leda a kasarsa, a shekarun baya dai danwasan ya bayyana ajiye takalman wasansa wa kasar Ajantina, daga bisani kuma ya dawo fagen fafatawa.

Dan wasan bayan Leicester mai shekara 25, Harry Maguire, yana dab da yarda da wata sabuwar yarjejeniyar da kungiyar kan albashin fan dubu 75,000 a ko wane mako.