Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan ranar ta 3 ga watan Mayu na ko wacce shekara domin duba irin rawar da 'yan jarida suke takawa domin ci gaban kasashen su da kuma fadakar da jama’a illolin hana kafafen yada labarai fadin gaskiya.
Wata kididdigar kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida ta nuna cewa a kowacce shekara 'yan jarida kan fuskanci matsaloli da dama da suka hada da muzgunawa wani lokaci ma har da kisa.
Wani dan jarida da ke aiki da jaridar Vanguard ta Najeriya mai suna Umar Yusuf, ya ce a wasu lokuta idan suka buga labaran da basu yi yiwa hukumomin tsaro dadi ba sukan gayyace su zuwa ofishin su domin su amsa tambayoyi, amma dai ba su taba daure shi ba.
Shima wani mai aiki da kamfanin dillanci yada labarain Najeriya, Yakubu Musa Uba, ya bayyana irin kalubalen da ya ke fuskanta a matsayin sa na dan jarida, da suka hada da rashin bada hadin kai musamman daga hukumomin gwamnati.
Ya kuma kara da cewa kamar su da suke zaune a arewa maso gabashin Najeriya, da zarar wani abu ya faru kamar abinda ya shafi Boko Haram da sauransu, idan sun kirawo hukumomin da abin ya shafa domin su tantance gaskiyar abinda ya faru don su bada labarin yadda yake sai ka ga suna kakkaucewa.
Sai dai wani dan jarida mai suna, Malam Shehu Adamu, ya ce daya daga cikin matsalar da 'yan jarida suke fuskanta shine rashin biyan su isasshen albashi, wannan yana daya daga cikin matsalolin da ya ke rage musu kwarin gwiwar fadin gaskiya komai dacin ta.
Sannan ya kara da cewa rashin isassun kayan aiki na zamani da kuma batun horar da su na cikin matsalolin da suke fuskanta, duba da yadda a kullum abubuwa ke canjawa a aikin jarida.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5