Ko An Yi Magudin Zabe Ba Zai Yi Muni Kamar da Ba

Tarzoma ta tashi bayan fashewar wani bom a Gombe

Ba'a taba zabe ba a Najeriya ba wata jam'iyya tayi korafin an yi magudi ko dauki dora ba

To saidai karfin adawa a wannan karon na son sauya ra'ayin masu sharhin kan lamuran siyasa.

Masu sharhin suna ganin ko an yi magudin ba zai yi muni ba sabili da taimakon naurar da hukumar zabe tace ta kawo na hana magudin.

Nasiru Gambo Malunfashi mai sharhi kan lamuran siyasa yace yanzu akwai wayewa ta 'yan Najeriya da wayewar masu neman kujeru ba kamar baya ba. Magudin, idan ma za'a yi, zai zama ya ragu sosai ba zai zama kamar na zabukan baya ba.

Amma wasu 'yan takarar kujerar gwamna musamman na APC irin su Inuwa Yahaya na ganin yarjejeniyar nan ta hana tarzoma domin gudanar da zabe cikin lumana bata tasiri a jihohi. Yace hakika an yi yarjejeniya tsakanin shugaban kasa da kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Janaral Buhari amma da yakamata an aika matsayin a kowace jihar kasar domin a aiwatar da ita sau da kafa.

Bisa ga yadda abubuwa suka wakana akwai kalubalen tsaro. Misali duk abubuwan da suka aukawa jam'iyyar APC sun aikawa 'yansanda, da SSS da duk sauran jami'an tsaro domin su san suna da matsala.

Yakamata a san cewa nemo canji ba abu ne mai sauki ba.Gwagwarmaya ce da dole za'a yita duk da wai za'a wahala. To saidai a karshen wahala akwai dadi. Kalubalen da APC ke fuskanta ramin da PDP ta fada ciki ne kuma shure-shure baya hana mutuwa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ko An Yi Magudi Ba Zai Yi Muni Kamar da Ba - 2' 36"