Rashin samun katin zaben dindindin da jama'a ke kuka da shi,ya kara bayyana karara a Abuja ma babban birnin tarayyar Najeriya, inda ake ganin bai kamata irin wannan matsala ta faru ba.
Hajiya Sadiya Aliyu ta yi awa tara a wani ofishin karbar katin zaben dindindin a Abuja, daga karfe takwas na safe har kusan karfe biyar na yamma, ta na wurin amma ba ta samu katin ta ba, haka ta koma gida.
Hajiya Sadiya Aliyu ta ce ina dalilin daukan buhunhunan katunan zabe akai wani wuri dake can cikin lungu, ta ce me ya sa ba a kai su inda kowa yayi rajistar zabe ba, a je a can a karba.
Hajiya Sadiya Aliyu ta ce idan ba gyara aka yi, har nan da watanni uku masu zuwa ma wasu 'yan Najeriya ba za su samu katunan zaben su ba.
A karshen tattaunawar Hajiya Sadiya ta baiwa hukumar zaben Najeriya shawarwari kan yadda za ta iya gyara wannan al'amari ciki mako daya kawai.
Ibrahim Alfa Ahmed ne ya tattauna da Hajiya Sadiya a ofishin Sashen Hausa na Muryar Amurka a birnin Abuja.
Cikin bacin rai da takaici Hajiya Sadiya ta yi bayani a cikin tattaunawar su da Ibrahim Alfa Ahmed a Abuja: