Rahotanni sun nuna cewar ‘yan Najeriya da dama ne suka shiga halin kaka nikayi, da dama kuma sun rasa rayukan su a sakamakon hatsaniyar da wasu ‘yan kasar suka tayar.
Wannan matsalar ta taso ne a yayin da masu rigimar wadanda ‘yan asalin kasar ne ke ikirarin cewa bakin sun mamaye masu wuraren ayyuka da kuma kasuwanci. Rahotanni sun nuna cewar wasu daga cikin bakin da suka rasa rayukan su, an kasha su ne ta wajan daurewa da sa masu wuta.
‘Yan Najeriya dai sun dade suna tururuwa zuwa kasar Afirka ta kudu. Koda shike akwai baki daga kasashe daban daban a kasar, amma rahotanni sun nuna cewra ‘yan Najeriyar kadai ne ke fuskantar wannan kalubale.
A wata hira da Usman Kabara, yayi da wani masanin harkokin kasa da kasa Mal, Ishak Kauran Mata yayi Karin bayanin cewar yakamata Najeriya ta shiga sahun sauran kasahen Afirka wajan kwashe jama’ar su dake zama a kasar da kuma zaunawa a dubi lamarin ta hanyar sharia da kuma doka da oda.
Your browser doesn’t support HTML5