An tuhumi wani dan sanda farar fata a jahar South Carolina ta Amurka da laifin kisan kai, bayan da wani hoton bidiyo ya nuna shi yana harba bindigarsa sau da dama a kan wani bakar fata, wanda ba ya dauke da makami, a yayin da yake kokarin tserewa.
Kisan da aka yi wa Walter Scott, mai shekara 50 da haihuwa, a ranar asabar da ta gabata a birnin North Chaleston, ya faru ne bayan da dan sandan mai suna Michael Slager ya tsayar da motar mamacin bisa dalilin yana tuki babu wutar burki.
Hoton bidiyon da wani mai shigewa ta gefen hanya ya dauka da wayar sa ta salula ya nuna yadda dan sandan ya harbi mamacin har sau takwas, bayan Scott ya fadi, hoton bidiyon ya kuma nuna yadda dan sandan ya sa masa ankwa sannan ya koma daidai wajan da ya fara harbin bakar fatar ya je ya dauko wani abu ya koma ya ajiye a kusa da gawar bakar fatar.
Mahaifin mamacin, Mr Scott ya fadawa shirin Today na giodan telebijin na NBC yau laraba cewar yayi imanin dan nasa “yayi kokarin tserewa ne saboda ba ya son a sake maida shi gidan kaso” sakamakon kin biyan kudin tallafin iyalin da yakamata ya biya “shiyasa ya ruga.”
Dafarko Slager yayi ikirarin cewa ya budewa Scott wuta ne bayan ya kama shi da kokowa ya dauke masa bindigar sa ta cilla wutar lantarki.
Wanda ya dauki hoton bidiyon da ba a bayyana ko waye ba, ya kaiwa iyalan Scott bidiyon. Lauyan iyalan Mr Scott ya kaiwa gidan jaridar New York Times wadda ta sa bidiyon a shafin intanet ran talata.
Lauyan iyalan Mr Scott, Chris Stewart, ya fadawa ‘yan jarida daren jiya talata cewa, “idan da ba a samu shaidar da ya dauki hoton bidiyon nan ba me zai faru? Da za a yi rufa-rufa ne domin rahoton farko da suka bayar shi ne cewa Mr. Scott ya kai farmaki kan dan sandan, ya kwace masa bindigar wutar lantarki zai yi amfani da shi a kansa, amma kuma ashe akwai wani yana ganin abinda ke faruwa.”
Hukumar Tabbatar da Bin Doka da Oda ta Jihar South Carolina, wadda it ace hukumar dake gudanar da ayyukan binciken aikata laifuka, ta fara bin diddigin wannan lamarin. Ita ma Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Tarayya, FBI, da kuma Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta Amurka duk sun fara gudanar da nasu binciken.
Wannan lamarin shi ne na baya-bayan nan inda ‘yan sanda fararen fata suke bindige bakaken fatar da bas u dauke da makami a Amurka. Irin wadannan lamurran da suka yi kaurin suna sun hada da bindige Michael Brown a garin Ferguson dake Jihar Missouri, da harbe Tamir Rice dan shekara 12 a Cleveland ta Jihar Ohio da kuma shake Eric Garner har lahira da ‘yan sanda suka yi a New York. Wadannan lamurran sun haddasa munanan matakan zanga-zanga a fadin Amurka kan yadda ‘yan sanda ke nuna halin babu sani babu sabo a yankunan bakaken fata da na ‘yan tsiraru.
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5