Rundunar ‘yan sanda a birnin Atlanta ta kori wani jami’inta farar fata daga aiki bayan da ya kashe wani bakar fata a lokacin da ya karbe wata na’urar wutar lantarki da ake amfani da ita wajen ladabtar da wanda ya nuna turjiya ga ‘yan sanda.
An harbe Rayshard Brooks ne a daren Juma’a bayan da ya karbe na’urar ya kuma yi yunkurin tserewa domin kada a kama shi da laifin da ake zargin ya aikata na yin tuki a cikin yanayi na maye.
Rundunar ‘yan sandan har ila yau ta dakatar da wani jami’inta na biyu daga zuwa aiki yayin da ake gudanar da bincike.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da shugabar ‘yan sandan birnin na Atlanta Erika Shields ta ajiye aikinta bayan kisan ba’amurken dan asalin Afirka - lamarin da ya janyo barkewar mummunar zanga zanga a birnin na Atlanta.
Zanga zangar dai ta faro ne cikin lumana a ranar Asabar amma daga baya ta jirkice ta koma tarzoma inda har masu boren suka datse babbar hanyar shiga birnin suka kuma kona kantin sayar da abinci na Wendy’s da aka kashe Brooks a farfajiyarsa.