A wani bangare na kokarin kawo karshen yawan kashewa da kuma sace mutane a jahar Zamfara, Sufeto-Janar na ‘yansandan Najeriya Mohammed Abubakar Adamu ya dakatar da hakar ma’adanai a jahar Zamfara da kuma duk wani abin da ya shafi harkar hako ma’adanai a jahar da kewaye. Sannan ya bayar da wa’adi ma duk wani dan kasar waje ke harkar hakar ma’adanai a Zamfara da ya tattara ya nasa ya yi gaba.
Wani kwararren kan harkokin yau da kullum mai suna Malam Yusha’u Aliyu, y ace ba a taba samun alaka tsakanin harkar hako ma’adanai a Najeriya da harkar ta’addanci ba. Ya ce akwai alaka ta jari hujja tsakanin masu hakar ma’adanai da masu saye da kuma ma’aikatan saboda haka babu yadda wani bangare zai so a karkashe talakawa masu aiklin ma’adanai. Ya kara da cewa a jahar Filato an jima ana hakar ma’adanai ba tare da an fuskanci irin abin da ke faruwa a Zamfara ba. Y ace akwai ma’adananmu a wasu sassan arewa amma ciki har da Kaduna da kuma Nasarawa amma, kamar yadda abin yak e a jahar Filato, ba a taba ganin masifa irin ta Zamfara a jahohin ba.
To amma wani masanin tsaro, Air Commodore Baba Gamawa (murabus) y ace ruwa baya tsami banza, bas hi yiwuwa bangaren tsaro ya dau irin wannan matakin ba tare da ya ga wasu bayanan sirri ba, wadanda, a cewarsa, ba lallai a bayyana ma sauran jama’a ba.
Da wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton: