A daidai lokacin da Kiristoci a fadin duniya ke ci gaba da bukukuwan Kirismeti wato ranar tunawa da haihuwar Yesu Almasifu, al’umar kirista a jamhuriyar Nijer sun sha alwashin ci gaba da yin addu'o'i kamar yadda hukumomin kasar suka umurta domin ganin cewa kasar ta samu dorarren zaman lafiya, duba da cewa har yanzu yan ta'adda na kai hare-hare su gudu zuwa iyakar Mali da Nijer da Burkina Faso.
Albarkacin ranar ta Kirsimeti, Pasto Assumane Abdu ya ce zasu ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya.
Shi ma Pasto Abubakar Musa cewa ya yi ba zasu fasa yin addu'o'i ba domin ba Nijer kadai ke fuskantar tashin hankalin ‘yan ta’adda ba har ma da wasu kasashen Afrika.
Haka suma kiristoci mata sun bi sahun mazan wajan ci gaba da yin addu'o'i su na neman sauki daga Allah don samun zaman lafiya a kasar da ma duniya baki daya.
Your browser doesn’t support HTML5