Kayayyakin masarufi sun yi tashin gwauron zabi a kasuwanni dake fadin Najeriya, musamman ma kasuwannin dake jahar Lagos, inda lamarin yafi tsanani kan kayan abinci wanda suka hada da Tumatiri zuwa Nama da Kaji kasancewar anfi amfani da su wajen shagulgulan bikin Kirsimeti.
Tsadar kayan masarufin na zuwa ne a wani lokaci da ake fama da komadar tattalin arziki a kasar. Wakilin Muryar Amurka dake jahar Lagos, Babangida Jibrin, ya zagaya wasu kasuwanni domin ganewa idanunsa yadda lamarin yake, inda ya zanta da masu zuwa sayayya da kuma ‘yan kasuwa.
Mutanen da Babangida ya zanta da su sun bayyana masa cewa kayayyaki sunyi tsada wanda hakan ke hana mutane iya sayen abubuwan da suka je saya a kasuwanni. Haka kuma a lokaci irin na Kirsimeti kasuwa kan cika makil, amma yanzu kam babu yawan mutanen da aka saba gani.
Akasarin mutane dai na alakanta tsadar rayuwar ne akan matsalar tattalin arziki wanda gwamnatin Mohammadu Buhari ta bullo da shi.
Sai dai kuma shugaba Buhari ya saka hannu na biyan kudin albashi da sauran kudaden ma’aikata na Naira Biliyan 71.8 na kasafin kudin shekara mai wucewa, lamarin da zai sa a biya ma’aikata albashinsu. Kawo yanzu dai akwai jahohi da ma’aikatun gwamnati da dama da basu karbi albashinsu ba, wanda hakan zai kawo tsaiko ga bukatunsu na sayan kayayyakin bikin Kirsimeti.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
n bayani.