La'akari da suma, sun soma azumin Ista na kwanaki 40, inda tuni suka soma nasu addu'o'in na neman samun zaman lafiya a wadannan kasashen, Kirista sun ce za su bi sahun 'yan uwansu Musulmi wajen bayar da gudunmowar tabbatar da zaman lafiya da zamantakewa mai falala.
Kirista a Jamhuriyar Nijer sun sha alwashin ba za a bar su a baya ba a wannan kasar wajen yi ma ta, da ma Najeriya addu'o'i, da hukumomin suka roka ga Musulmi a cikin wannan watan na azumin Ramadan domin kasar ta samu salama da zaman lafiya tare da makwabciyarta. Duba da yanda matsalolin tsaro suka kai wa wadannan kasashen halin intiha.
Kiristan sun ce sun soma bada umurci a Coci - Coci a wannan lokacin da suma suke yin azumin Ista na kwanaki 40, domin rokon Allah ya kawo zaman lafiya mai dorewa a Nijer da Najeriya, kamar yanda Pasto Abubakar Musa, daya daga cikin mambobin kungiyoyi na kasar Jamhuriyar Nijer na kirista ya bayyana.
Suma Musulmin kasar sun yi marhabin da jin wannan labarin, inji Liman Amadu mashawarci ga kungiyar CEDIR ta hadin kan mabambanta addinai ta gundumar Birnin N'Konni.
Samun hadin kan Musulmi da kirista a kan wannan lalura ta tsaro a kasa kamar jamhuriyar Nijer, maluman bangarorin guda biyu na cewa, ba karamin tasiri abin zai yi ba wajen samun taimakon Allah don ganin an barranta daga wannan matsalar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5