Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Addu'a Kan Rashin Tsaro Ta Fara Tasiri A Najeriya-JNI


Kimanin watanni biyu da bada umarnin addu'o'i na musamman da kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta yi, Kungiyar ta ce ana samun nasarori game da matsalolin tsaro a Najeriya sai dai kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce gwamnati na bukatar kara damara idan tana son magance matsalar tsaro.

Babban sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam JNI na kasa, Dr. Khalid Abubakar Aliyu wanda ke karin bayani game da addu'o'in da kungiyar ta bada umarni ya ce har yanzu ba a daina addu'ar neman mafita game da matsalar tsaron ba.

Ita kuwa kungiyar Kiristoci ta kasa reshen jahar Kaduna, ta bakin shugaban kungiyar, Rabaren Joseph John Hayeph, cewa ta ke har yanzu akwai sakaci a bangaren gwamnati game da matsalar tsaro.

A nashi bayanin, Imam Abdulkadir Hashim shi ma ya goyi bayan cewa, akwai sakaci a lamarin. Bisa ga cewarsa, alhakkin tsaro ya rataya a wuyan gwamnati ne da kuma al'umma baki daya.

Dama dai ta'azzarar matsalar tsaro a Najeriya ce ta sa kungiyar Jama'atu Nasril Islam bada umarni addu'o'i kuma cikin watanni biyun da aka yi, ta ce sauyi ya fara samuwa.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG