Wata kungiyar kasa-da-kasa me suna Grassroot Anticorruption Initiative mai yaki da cinhanci da rashawa, da almundahanar dukiyar jama’a, ta bukaci kungiyoyi da hukumomin duniya da su gudanar da bincike, tunda dai al’amarin ya shafi kasashen Najeriya da Afrika ta kudu a kan kudade da kasar ta Afrika ta kudu ta chapke a hannun wasu ‘yan Najeriya.
Kakakin wannan kungiya Ahmad Dauda yayi nuni da cewar tunda dai shugaban kasar Najeriya ko hukumar nan me yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC da ICPC basu dauki wani matakiba, to yakamata kungiyoyin duniya su fito don yakar wannan al’adar. Ya kara da cewar idan har anason shugabancin adalci to sai an samar da shuwagabannin na gari.
Shima wani dan gwagwarmaya Kwamrade Sale Taki yayi kira ga hukumar yaki da almundahanar kudi ta majalisar dinkin duniya da ta binciki wannan lamarin don sama ma al’umar Najeriya sauki.
Your browser doesn’t support HTML5