Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Takardun Shiga Neman Tsayawa Takara a Jam’iyyun Najeriya


PDP
PDP

‘Yan siyasar Najeriya na cigaba da kokawa kan tsadar takardun shiga neman tsayawa takara a jam’iyyar PDP mai mulkin kasar da kuma jam’iyyar hamayya ta APC, yayin da a hannu guda kuma masana kimiyyar siyasa ke ganin matakin ka iya tauye hakkin ‘yan kasa na shiga a dama dasu a fagen demokaradiyya.

A wani jaddawali da jam’iyyar APC ta fitar ‘yan makonnin dasuka gabata ya nuna cewa mai neman takarar majalisar tarayya zai karbi takardar neman sha’awar ne akan Naira miliyan biyu, Sanata kuma zaibiya Naira miliyan biyar da doriya, yayinda gwamnan jiha zaibiya sama na Naira miliyan goma, mai neman takarar ‘dan majalisar dokoki na jiha zai biya Naira dubu dari takwas, yayin da mai neman takarar shugaban kasa zai yanki takardar sha’awar nuna takarar akan kudi Naira miliyan ashirin da bakwai.

Wani dan jam’iyyar APC a jihar Kano Mallam Muhi Magaji, yace “ yanzu a yau danake gayama a kwai mutum indan ka tsaidashi zabe a mazabarsa zai iya cin zabe, amma dun da aka haife shi baita’ba ganin Naira miliyan ba ballema yanemo maka Naira miliyan biyu, shiyasa suke hanawa ayi zabe na shugabanni shiyasa suke hana duk wanda zai shigo ya zamana yana cikin wanda zasu juya akalar jam’iyya, su hana kowa shiga sai yaransu, kamar yadda akasa wanna kudun jam’iyya tazama ta ‘yan jari hujja sai wanda keda kudi zai iya shiga.”

Itama Jam’iyyar PDP nata kudaden data fitar na sayan takardar sha’awar tsayawa takara basu da banbanci dana takwaratta ta APC, tabakin wani jigo magoyin bayan Jam’iyar PDP a Kano Kwamaret Sa’idu Bello, yace “ cin zarafine ga demokaradiyya ace an tsawwala kudin da zaka sayi takardar da Jam’iyya zata barka kayi takara, wanan yana kashe zaben mutum nagari wanda zai amfanawa al’umma.”

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG