Kimanin Rumfuna 80 Ne Suka Kone A Kasuwar Kurmi - Hukumar Kashe Gobara A Kano

Wani sashe da gobara ta lashe a kasuwar Kurmi da ke jihar Kano, Najeriya

Wani sashe da gobara ta lashe a kasuwar Kurmi da ke jihar Kano, Najeriya

A makon jiya ma gobara ta lalata dukiyar ‘yan kasuwa ta biliyoyin Naira a kasuwar Monday Market ta birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a Najeriya ta tabbatar da cewa, wuta ta kona rumfuna kimanin 80 a Kasuwar Kurmi dake tsakiyar birnin Kano, bayan da gobara ta tashi a kasuwar a jiya da daddare, har zuwa sallar Asuba.

Gobarar ta tashi ne a bangaren masu sayar da kayan kwallliya, kamar turaruwa da sauran kayan kawa na mata, kana daga bisani ta fantsama zuwa sashen masu kayan kamshi, irin su Citta da kanunfari.

Kayayyakin na miliyoyin Naira ne dai suka kone kurmus, kamar yadda kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi ya shaidawa Muryar Amurka.

Ya ce, da misalin karfe hudu na asuba ne Jami’an hukumar suka sami kiran gaggawa ta wayar tarho , inda aka sanar dasu tashin gobarar kuma nan take suka garzaya domin kai dauki.

Saminu Abdullahi ya yi bayanin cewa, jami’an sun yi nasarar kashe wutar cikin karamin lokaci, ko da yake, kafin zuwan su ta lalata dukiya ta daruruwan miliyoyin Naira.

A cewarsa, bincike ya yi nisa wajen kokarin gano musabbabin tashin gobarar.

Kasuwar Kurmi dai itace kasuwa ta farko a birnin Kano, wadda ta kwashe daruruwan shekaru da kafuwa.

A makon jiya ma gobara ta lalata dukiyar ‘yan kasuwa ta biliyoyin Naira a kasuwar Monday Market ta birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.