Kimanin Rabin Matasa Sun Shaku Da Wayoyinsu A Kasashen...

Matasa da wayoyinsu

Kimanin rabin matasan dake Amurka da Japan sunce sun shaku da wayoyinsu na zamani.

Wasu masu bincike daga jami’ar Kudancin California (USC), sun yiwa matasan Japan kimanin 1,200 tambaya kan yadda suke amfani da kayayyakin fasahar zamani.

Masu binciken sun kwatanta bayanan da suka samo a Japan da wanda a baya suka samu a Arewacin Amurka.

A cewar shugaban sashen makarantar sadarwa da aikin jarida, Willow Baya, ta ce ci gaba da aka samu a fannin fasaha, na canza yadda mutane ke mu’amala da juna, ba kuma kadai a fadin duniya ba, har ma da mutane da ake da kusanci da su.

Binciken dai ya nuna cewa kashi 50, cikin 100, na matasan Amurka da kuma kashe 45, cikin 100, na matasan Japan sun bayyana yadda suka shaku da wayoyinsu.

Kaso 61, cikin 100, na iyayen matasa a Japan sunyi imanin cewa yaransu sun shaku da wayoyinsu, idan aka kwatanta da kashi 59, na iyayen matasan Amurka wadanda aka yiwa tambayar.

Kusan matasa 7, cikin 10, ne sukace da zarar an aiko musu da sako ta wayoyinsu suna jin zumudin karantawa su mayar da amsa, idan aka kwatanta da kusan rabin matasan Japan.

Your browser doesn’t support HTML5

Kimanin Rabin Matasa Sun Shaku Da Wayoyinsu A Kasashen - 1'22"