Kimanin Mutane Miliyan Biyu Ne Suka Fito Zanga-Zanga a Hong Kong

Hong Kong

Titunan kasar Hong Kong sun sake cikewa makil da dubban daruruwar masu zanga zanga saye da babbakun kaya a jiya Lahadi domin kalubalantar kudirin nan da zai bada dama a mika masu laifi ga China.

Masu zanga zangar sun hana gudanar da harkokin kasuwanci kana suka sa ayyukan hukumomin gwamnati suka tsaya cik, yayin da wadanda suka shirya macin suka ce mutane miliyan biyu ne suka bazu a kan tituna.

An gudanar da wannan zanga zangar ce wuni guda bayan da shugaban kasar Carrie Lam ta dakatar da aiki a kan kudirin amma masu zanga zangar sun ce zasu ci gaba da bore har sai an janye batun kudirin kwata kwata.

A halin da ake ciki kuma, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce shugaba Donald Trump yana shirin tattauna batun Hong Kong da takwarar aikinsa na China Xi Jinping a taron kolin manyan kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya a kasar Japan.