Kimamin Mutane Dubu Dari Biyu 'Yan Nigeria Da Mali Suke Gudun Hijira a Jamhuriyar Niger

Hukumar UNHCR ta MDD dake kula da 'yan gudun hijira

Babban daraktan hukumar UNCHR dake kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Fillipo Grandi yace akwai yan gudun hijira kimanin miliyan 68.5 saboda karuwar rigingimu a duniya

Mutane sama da dubu dari biyu ‘yan Najeriya da Mali suka ketara Jamhuriyar Nijar a shekarar 2012 da nufin samun mafaka a yankin Diffa sanadiyar rikicin Boko Haram. Haka ma wadanda suke gudun hijira a yankunan Tilaberi da Touha sun isa wuraren ne bayan barkewar yaki a arewacin Mali.

Albarkacin ranar gudun hijira ta duniya hukumar UNHCR ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta shirya wani baje kolin kayayyaki a Birnin Yamai inda aka sanar da duniya cewa kawo yanzu akwai ‘yan gudun hijira kimanin miliyan 68.5 a duk fadin duniya.

A wurin baje kolin wani dan Mali dake gudun hijira a Nijar ya ce ya yi shekara 6 a kasar duk da cewa yana son ya koma kasarsa amma babu hanyar yin hakan. Yana samun aiki kadan kadan yana yi amma yana rokon Allah ya kawo karshen matsalar da ta fitar dashi daga kasarsa kana ya koma. Haka ma Usman Maude ya ce tashin hankali, da kashe kashe suka rabashi da kasarsa.

Bayanai sun nuna cewa matsalar ‘yan gudun hijira matsalar ce dake ci gaba da habaka, idan aka yi la’akari da yadda ‘yan gudun hijiran ke karuwa kowace shekara sanadiyar yake yake da tashin hankali dake kara barkewa kamar yadda babban daraktan hukumar UNHCR Fillipo Grandi, wanda yake ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar, ya bayyana a ranar ‘yan gudun hijira.

Fillipo Grandi y ace a bara an kiyasta cewa ‘yan gudun hijira miliyan 66.5 ake dasu a duniya amma a bana an gano adadinsu ya h aura zuwa miliyan 68.5 sanadiyar rashin samun nasarar warware rigingimun da ake fama dasu. Misali a shekarar 2017 rikicin kasar Gambia ne kawai aka yi nasarar magancewa.

Malam Zubairu Musa wani dan jarida da ya saba ziyartar ‘yan gudun hijira, yace mata da yara kanana su ne suke shan wahala saboda cikin miliyan 68.5 mafi yawansu mata ne da yara. Idan yara suna cikin halin gudun hijira basu da damar su je karatu. Malam Musa yace ya kamata a duba a ga irin matakan da za’a dauka domin kare mata da yara.

Shi ma Bubakar Sido jami’in hulda da jama’a na hukumar UNHCR reshen Nijar y ace yakamata a dubi hanyoyin da za’a taimakawa ‘yan gudun hijra da bakin haure da kasashen dake da niyyar taimaka masu, irin su Nijar

A saurari rahoton Souley Mamman Bako domin karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar ‘Yan Gudun Hijira – 5’ 39”