Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Fiye Da Miliyan 152 Ke Bauta A Afrika


Yara A Afrika
Yara A Afrika

Yayinda a yau 12 ga watan Yuni kasashen duniya ke bukin tunawa da ranar yaki da bautar da yara kungiyoyin kare hakkin yara kanana a jamhuriyar NIJER sun shawarci gwamnatin kasar ta kara jan damara domin tunkarar wannan matsala dake neman turjewa matakan da aka dauka a can baya da nufin takawa wannan mumunar dabi’a burki.

A shekarar 2002 ne Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar tayar da kungiyoyi da gwamnatoci daga bacci akan bukatar karfafa ayyukan ganar da jamaa illolin dabiar bautar da yara, yanzu haka yara miliyan 152 ne ke fama da wannan matsala dalilio kenan da aka karkatar da shagulgulan ranar ta bana ga ayyukan wayar da kai akan bukatar kula da lafiyar yara tare da karesu daga hadarin da ke da nasaba da dalilan aiki.

Nijar na daga cikin kasashen da suka dade da amincewa akan maganar yaki da bautar da yara kokuma sanya yara aikin da yafi karfin su, alamu na nuna cewa haryanzu akwai sauran aiki, dalili kenan da kungiyoyi irin su ALTEN suka fara yunkurin ankarar da gwamnatin kasar abubuwan da ke faruwa dan ganin an fito da wasu sabbin dabaru.

kungiyar kwatago ta duniya ta sanar cewa nahiyar Afrika ce kan gaban yankunan da aka fi bautar da yara a duniya yayin da aka gano cewa daga cikin miliyan 152 da ke cikin wannan hali, kashi 70.9 na aiki a fannin noma sai kuma fannin masana'antun dake bautar da kashi 11.9 yayin da kashi 17.2 suke cikin wani hali a ma'aikatun bariki .

Ga Rahoton Sule Mummuni Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG