Kimanin Mutane 2000 Ke Mutuwa A Duk Shekara Sanadiyar Cutar Daji A Najeriya

Watan Oktoba wata ne da aka ware domin fadakar da mata game da illar cutar daji ko cancer, musamman wanda ke kama mata a mama ko mahaifa, saidai kuma ba dukkanin matan ko jama’a ne keda masaniya da wannan kokari da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu keyi ba.

Bayanai na hukumar lafiya ya nuna cewa kimanin mutane dubu sabain da biyu ne ke mutuwa sakamakon cutuka dake da nasaba da cutar cancer kokuma daji. A yayinda a Najeriya, a kowacce shekara ake samun mutane dubu biyu dake rasa rayukansu a dalilin cutar ta daji. Cutar daji ta mama ko ta mahaifa ita ke kashe mutane kashi hamsin da biyu cikin dari a al’ummar Najeriya.

Uwar gidan gwamnan jihar Ondo Mrs Betty Akeredolu, itace shugabar wata kungiya mai zaman kanta dake fadakar da mutane akan cutar ta cancer, kuma ta bayyana cewa wannan cuta idan aka hada mutuwar da take haddasawa yafi wanda ake dashi ta bangaren HIV da malaria da tarin fuka.

A shekaru ashirin da suka gabata ita kanta ta samu warkewa daga cutar ta cancer dalilin da yasa ta kafa wannan kungiya domin fadakar da mata da sauran alumma game da illar dake tattare da wannan cuta. Bayan ita kanta akwai matan gwamnoni guda biyu, matar gwamnan jihar Neja da gwamnan Jihar Kebbi da suka tashi tsaye wajen yaki da cutar ta cancer.

Wani likita Maku Sidi, ya bayyana cewa ita cancer sinadarai ne a cikin sashin jikin mutun da yake ci gaba da tsiro kuma in aka tarbeshi da wuri ana iya magance shi ba tare da bata lokaci ba, amman in ya kai wani sashi da wuyar warkarwa. Wata matsala da masana kiwon lafiya ke fuskanta shine rashin fadakarwa da kuma jahiltar wannan cuta inda ake cewa batajin magani. hasashen da likita ya musanta.

Your browser doesn’t support HTML5

Kimanin Mutane 2000 Ke Mutuwa A Duk Shekara Sanadiyar Cutar Daji -3'44"