Kimanin mata dubu hamsin da biyar suke mutuwa a shekara lokacin haihuwa a Najeriya

Wata mai jego da ta haifi 'yan uku a wani asibiti na birnin Ikko

Shugabar kungiyar Likitocin Najeriya Dr, Princess Campbell ta bayyana cewa Najeriya na matsayin na 176 daga cikin kasashe 190 na duniya da suka ci gaba a fannin harkokin kiwon lafiya.

Shugabar kungiyar Likitocin Najeriya Dr, Princess Campbell ta bayyana cewa Najeriya na matsayin na 176 daga cikin kasashe 190 na duniya da suka ci gaba a fannin harkokin kiwon lafiya.

Bisa ga cewar shugabar kungiyar likitocin, ana rasa ran mace daya daga cikin mata goma sha takwas sakamakon matsalolin da suka shafi haifuwa. Dr Campell ta bayyana haka ne a wajen wani taron da kungiyar tayi kan matakan shawo kan mace macen mata masu ciki a dakin taro na Civic Center dake birnin Ikko.

Rahoton asusun tallafawa kananan yara na UNICEF na nuni da cewa, mata a kasasahe masu tasowa kamar Najeriya suna cikin hadarin mutuwa sakamakon matsalolin da suka shafi haihuwa kimanin sau dari uku fiye da wadanda suke kasashen da suka ci gaba. Dr Campbell ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara maida hankali wajen kula da harkokin kula da lafiya musamman ta mata masu ciki.

An yi kiyasin cewa kimanin mata dubu hamsin da biyar ke mutuwa kowacce shekara a lokacin haihuwa ko kuma ta dalilin matsaloli da suka samu bayan haihuwa. Ta kuma yabawa kungiyoyi masu zaman kansu da suke bada gudummuwa a yunkurin shawo kan wannan matsalar.