Kididdiga ta nuna cewa ana samun mata kimanin dubu dari uku dake dauke da juna biyu a jihar Sokoto kadai a kowace shekara, sai dai kashi ashirin da biyar bisa dari na wannan adadin ne ke zuwa asibiti domin awon ciki yayi da kuma kashi biyar bisa dari ne kacal na wanna adadin suke haihuwa a asibiti.
Wannan lamari yana kara yawaitar adadin mutuwar mata a lokacin haihuwa, abinda kuma yake kara damun gwamnatin jihar ta Sokoto.
Hakan yasa ma’aikatar lafiya ta jihar Sokoto, fitowa da hanyoyin fadakar da mata masammam sababbin aure ta hanyar ta hanyar wani gagarumin fadakarwa da ya kunshi mata, ‘yan mata da iyaye maza da mata da ungozomomi, wanzamai dama jami’an kiwon lafiya, wanda aka yiwa taken “ Kakar Aure Can Take Sallah”
Dr. Balarabe Shehu Kakale, kwamishinan kiwo lafiya na jihar Sokoto, yace watan Shaaban shine watan kakar aure kamar yadda kowa ya sani shi yasa ma’aikatar lafiya da na harkokin mata ta kudiri a niyyar tabbatr da ganin cewa an ilimantar da mata kan abinda ya shafi haihuwa da lafiyarsu.
An gudanar da taron gangamin ne tare da hadin guiwar ma’aikatar harkokin mata da yara kanana ta jihar.
Kwamishiniyar ma’aikatar harkokin mata Hajiya Kulu Sifawa, tace wannan taron ai yi shine saboda akara tunatar da Mata muhimmancin su ga al’uma.
Your browser doesn’t support HTML5