Kimamin mutane dubu goma mahaukaciyar guguwar teku ta kashe a Philippines

Hotunan gidajen da mahaukaciyar guguwar teku ta lalata a kasar Philippines.

Jami'an lardunan da mahaukaciyar guguwar teku Haiyan ta yiwa barna a kasar Philippines, sunce tana yiwuwa guguwar ta kashe kimamin mutane dubu goma. Yau Lahadi yan sanda da jami'an yankin suka gabatar da wannan kiyasi bayan da suka nazarci irin barnar da guguwar tayi a lardin Leyte inda aka baiyana cewa guguwar tayi barnar sosai.
Jami'an lardunan da mahaukaciyar guguwar teku Haiyan ta yiwa barna a kasar Philippines, sunce tana yiwuwa guguwar ta kashe kimamin mutane dubu goma.

Yau Lahadi yan sanda da jami'an yankin suka gabatar da wannan kiyasi bayan da suka nazarci irin barnar da guguwar tayi a lardin Leyte inda aka baiyana cewa guguwar tayi barnar sosai.

Shugaban 'yan sandan yankin yace yawancin mace macen su faru ne a sakamakon rushewar gine gine da kuma wadanda ruwa ya cinye.

Sakataren harkokin cikin gidan Philippines Mar Rixos yace da wuya a baiyana irin barnar da guguwar tayi a Tacicban, baban birnin Leyte.

Kamfanin dilancin labarun Associated Press ya bada labarin cewa, kantoman garin ya fadawa 'yan jarida cewa an gano gawarwarki kimamin dari hudu.

Mahaukaciyar guguwar teku mafi karfi da aka taba gani data apkawa kasar, tazo ne da iskar dake juyawa ko gudun kimamin kilomita dari uku cikin sa'a guda.

Yanzu dai wannan guguwar ta doshi kasar Vietnam inda masu hasashen yanayi suka ce ana sa ran ta isa kasar yau Lahadi da dare ko kuma gobe litinin idan Allah ya kaimu.

Hukumomin kasar Vietnam sun kwashe dubban mutane daga yankunan gabar teku, inda tuni dosowar guguwar ta hadasa iska mai karfi da igiyar teku.

Jami'ar dake kula da taimakon gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos tace tuni aka tura jami'an Majalisar domin nazarin irin barnar da guguwar tayi.

Waje daya kuma baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yiwa yan kasar ta'aziyar wadanda suka mutu, yana mai fadin cewa, rashin da aka yi ya sosa masa rai sosai.