Kerry Ya Kai Ziyara Mongolia

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Yana Jawabi Yayin Ziyararsa a Mongolia

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Yana Jawabi Yayin Ziyararsa a Mongolia

Sakataren harokokin wajen Amurka, John Kerry, ya isa birnin Beijin bayan da ya kai wata ziyara a Mongolia, ziyarar da ta sha banban da irin wadanda ya ke kaiwa, wacce kuma ita ce ta farko da ya kai a matsayinsa na babban jami’in Amurka.

A yau Lahadi, Kerry ya kwatanta kasar ta Mongolia a matsayin “indararo ko kuma bulbular dimokradiya” wacce ke kewaye da jam’iya guda da gwamnatocin Rasha da China ke tasiri akanta.

A shekarar 1987, Amurka ta hada huldar diplomasiya da Mongolia, kuma hukumomin Washington suna taimakawa fagen siyasar kasar da kuma fannin bunkasa tattalin arzikinta.

Sai dai ana dasa alamar tambaya kan batutuwan kare dimokradiya da hakkin bil’adama a kasar ta Mongolia, inda wani rahoton ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya nuna damuwa kan rashin kwararan dokoki da nuna gaskiya wajen samar da dokokin, da kuma yadda bangaren zartarwa ke gudanar da ayyukansa ba bisa ka’ida ba.

A cewar ma’aikatar harkokin wajen ta Amurka, Kerry ya kaddamar da wani sabon shirin a karkashin hukumar nan ta bunkasa kasashe ta Amurka, wato USAID.