“Ina tare da fitattcen mawakin Gambarar Amurka Kenye West, wanda yanzu ya kawo mana ziyara. Ina masa fatan jin dadin ziyarar.” Shugaba Moise ya kafe a shafin Twitter.
Wannan sanarwa wadda ta hada da hotuna hudu, sun nuna shugaban kasa Moise da Kenye West sanye da takunkumi a fuskokinsu.
Ba a san dalilin wannan ziyara da Kenya ya kai kasar dake yankin Karabiyan. Sai dai shi bai kafe komai ba a shafinsa Twitter @kanyewest ba.
Kamar yadda kafofin labaran yankin suka bayyana, shahararren mawakin ya sauka kasar Haiti ne ranar Juma’a da safe, ya kuma hadu da shagaban kasar wanda ya zagaya da shi wasu kyawawan tsibiri biyu da ke yawan zuwa yawon bude ido.
Kenye West ya sanar da tsayawarsa takarar shugaban kasar Amurka ranar 4 ga watan Yuli na 2020, a hukumance kuma zai fito a takardun kuri’un zaben watan Nuwamba a jihohin Amurka 11.