Kenya: Wasu Musulmi Sun Kare Kiristoci daga Halaka

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Ahalinda ake ciki kuma, wasu fasinja musulmi, da 'yan binidga da ake zargi masu tsatsauran ra'ayin addinin Islama suka yiwa Bas da suke ciki kwanton bauna a Kenya, sun kare abokan tafiyarsu kiristoci, sun ki amincewa da umarnin 'yan binidgan cewa su kasu gida biyu bisa addininin da suke bi.

Mutane biyu sun halaka a harin da aka kai a yankin karamar hukumar Mandera dake arewacin kasar, lokacinda 'yan binidga da aka hakikance 'yan kungyiar al-shabab daga Somalia ne, suka bude wuta kan motar.

Shaidun gani da ido suka ce wasu fasinjojin musulmi suka baiwa abokan tafiyarsu kiristoci hijab ko nikab domin boye kamaninsu, watakil sun tuna da wani hari da aka kai a wannan yankin a bara, sa'ilinda 'yan binidgan al-Shabab suka kashe mutane 28 wadanda ba musulmi ba, wadanda suka tilastawa fita daga cikin motar kasuw a da suke ciki.

Jami'an gwamnatn da suke yankin suka ce, maharan sun tilastawa kowa dake cikin motar ya sauka, kuma su shiga layi biyu, daya na musulmai guda kuma na wadanda ba musulmi ba. Duka fasinajojin suka ki, suka cewa 'yan bindigan ba zasu yi ba, idan suna son, su kashe su dukkansu.

Daga bisani maharan suka tafi, bayan da fasinjojin suka nuna hadin kai.