KENYA: Barayin Dabbobi Sun Kashe Mutane 54

Tunawa da ahre-haren Kenya

Barayin dabbobi sun kashe mutan 54 sun kuma raba wasu 350 da gidajensu

Wasu mutane da ake kyautata zaton barayin shanu nesunyi kwanton ‘bauna suka kashe akalla mutane 54 a wani ‘kauye dake arewa maso yammacin Kenya,kana suka sace daruruwan dabbobi.

Hukumarbada agajin gaggawa taRed Cross ta yankin tace, kusan mutane 350 aka kora daga gidajensu.

Jami’an tsaron ‘yan san dai sunce harin ya fara ne ranar Litinin, lokacin da wasu ‘barayi suka kaiwa wani ‘kauye hari suka sace dabbobinsu, suka kashe mutane bakwai. Mutanen kauyen kuma suka kai harin ‘daukar fansa.

Satar dabbobi da kuma fada tsakanin manoma da makiyaya abu ne da ya zama ruwan dare gama gari ayankunan gabashin Afirka, al’amarin damasana suka ce ya kara zama hadarin gaske saboda kabilun dake ‘bangaren sunaamfani da bindigog yayin da suke noma. Yawancin sabbin makaman dai sun gaje sune daga fadace fadacen da ake yi a Sudan da Uganda, yayinda sauran makaman kuma wasu ‘yan sandan wucin gadi na Kenya ne suka mallakesu tun fil azal.