Kebbi: Bagudu Zai Binciki Dakin Gari

EFCC

Bayan da aka rantsar da gwamnoni a jahohin Najeriya, yanzu haka wasu daga sabin gwamnoni na shirye shiryen gudanar da binciken gwamntocin da suka shude, kamar yadda ya ke faruwa a jahar Kebbi.

Sabon gwamnan Jahar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya ce gwammnatinsa ta gaji bashin naira biliyan 83 daga gwamnatin Sa’idu Nasamu Dakin Gari.

Rahotanni daga jahar ta Kebbi na cewa yanzu haka an kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Kwaido domin binciken gwammnatin da ta shude tare da bin bahasin bashin da ta bari.

“Sai yau ne Allah ya ba da dama gwamntin da ta shude ta bamu takardu, don haka sai mun duba takardun nan mun ga abin da jaha ta ke ciki domin mu gayawa kowa abin da ake ciki.” Inji Bagudu.

A cewar sakataren watsa labaran jam’iyyar APC a jahar ta kebbi, Alhaji Sani Dodo, an barwa gwamna Bagudu “bashin dala biliyan 21 sannan an bar mishi bashin biliyan 47 na ayyukan da aka shata sannan sai ayyuka wadanda aka sakawa hanu cewa an yi su amma ba a ko fara ba na zunzurutun kudi naira biliyan 15.”

Dodo ya kara da cewa za su bincike yadda aka ciwo bashin da me aka yi da kudin sannan su waye suka ciyo bashin.

Wakilin Muryar Amurka ya tambayeshi shin ko ba za a musu kallon cewa wannan shirin bita da kulli ba ne akan gwamnatin da ta shude, sai Dodo ya ce abin da ake so a yi bin hakki ne.

“Ai neman hakki ba bita da kulli ba ne, kamata ya yi a lokacin da zai sauka ya ce ni Sa’idu Nasamu Dakin Gari na iske kudi kamar haka na samo kudi kamar haka sannan na kashe kamar haka, sannan ga abinda na rage.

Da wakilin Muryar Amurka Murtala Faruk Sanyinna ya nemi jin ta bakin gwamnatin da ta shude, ya kuma tuntubi kwamishinan kudi Bello Muhammadu Tuga ta wayar talho, wanda ya ce ba shi da hurumin ya yi magana a kai.

Wannan dai tamkar tarihi ne ya maimaita kansa, domin shima Dakin Gari ya kafa wani kwamiti makamancin wannan da ya binciki gwmanatin Adamu Aleiro da ya maye gurbinsa.