Gwamna Kashim Shettima ya yabawa sojojin ne yayin da ya kai ziyara garin Bama daya daga cikin garuruwan da suka kwato daga hannun kungiyar Boko Haram.
Gwamnan yace abun yabawa ne matuka bisa ga gagarumin kokarin da suka yi tare da taimakon kungiyoyin sa kai da 'yan gora kato da aka sani da lakabin "Civilian JTF".
Gwamnan yace akwai bukatar taimakon gaggawa ga garuruwan da aka kwato domin wasunsu kamar Bama an kone kusan kashi casa'in cikin dari. Babu komi na jin dadin rayuwa. Ma'aikatu da makarantu da ma gidan Shehun Bama duk an konesu kurmus.
Kashim Shettima ya roki gwamnatin tarayya da ta taimakawa garuruwan da tallafawa al'umominsu da suka tagayyara suka kuma fada cikin halin kakanikayi.
Gwamnan ya kai ziyara Gubio garin da 'yan Boko Haram suka kai hari baya bayan nan inda ya jajanta masu da yi masu alkawarin tallafa masu. Wasu mutanen garin sun bayyana yadda 'yan ta'adan suka shigo garin suna harbe-harbe kafin su ma su mayarda martani har suka samu suka kashe da dama cikinsu.
A wani halin kuma Shehun Bama Alhaji Kyari Umar Ibn El-Kanemi ya roki gwamnatin jihar ta taimaka wajen tallafawa al'ummarsa da yanzu suke a warwatse cikin gidajen 'yanuwa da abokan arziki.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.