Tsadar rayuwa a Najeriya ta zama tamkar ruwan dare gama gari kamar yadda wakilin Muryar Amurka a jihar Bauchi ya jiwo mana.
Wani Malam Aliyu Muhammad mazaunin garin Bauchi fadar gwamnatin jihar yace a halin da ake ciki yanzu kusan kashi saba'in cikin dari basa cin abinci sau uku kamar da saboda mugun tsadar kayan masarufi.
Yace sabulun da za'a saya ya yi tsada. Burodi ya yi tsada. Shinkafa ta yi tsada. Man gyada ya yi tsada. A baya ana sayar da kwalbar man gyada nera dari biyu ne amma yanzu ta haura zuwa dari biyu da hamsin. Yace suna tunanen Buhari shugaba ne nagari amma ba dan siyasa ba ne.
Dangane da samarda kayan masarufi gwamnatin yanzu ta Buhari bata da manufofi masu kyau. Ita bata kawo kayan masarufi ba kuma ta toshe hanyoyin shigo dasu . Dole 'yan kadan dake kasar farashinsu suka yi tashin goron zabi.
Malam Aliyu yace dole a fito a fadawa Shugaba Buhari gaskiya cewa 'yan Najeriya fa suna shan wahala a karkashin gwamnatinsa.
Wani ma'aikacin gwamnati yace rashin daidaiton albashi ya sa ma'aikatan gwamnati na shan wahalar sayen kayan da suke anfani dasu yau da kullum domin kasuwa daya ce kowa ke zuwa. Yakamata gwamnati ta duba ta daidaita a'lamarin.
A cewar Malam Abdullahi Yalwa wani masanin tattalin arziki yace wannan lokaci ne da ake bukatar sadaukar da kai daga kowa a duk fadin kasar. Yakamata jama'a su sani canjin da ake bukata zai kawo kuncin rayuwa na wani dani lokaci. Ba za'a cigaba da rayuwar shaholiya ba. Duk abun alheri sai an sha wuya kafin a sha dadi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5