Hanyoyin da za a iya magance matsalolin Najeriya shine kawas da kabilanci, bam-bancin addini, da sauransu musamman yanzu da ake shirin yin zaben shekarar dubu biyu da goma sha biyar.
WASHINGTON, DC —
Masanin harkokin nazarin rayuwar dan‘adam da binciken hanyoyin kawo hadin kai da fahimta tsakanin al’umma dake wata jamia’a a Amurka, farfesa Samuel Zalanga, yace akwai bukatar jama’ar Najeriya su kawas da banbance-banbancen dake tsakanin su domin ciyar da kasa gaba, yayi wannan kalamin ne a wata a hira da yayi da muryar Amurka.
Farfesa Zalanga yace, magance matsalolin zabe a kasar shine iya gano hanyoyin da ya kamata a bi ta wajen duban makamantan wadannan matsalolin da suka faru a duniya, ya kuma yi kira ga talakawan Najeriya da su kawas da duk wani bambanci musamman na addini, kabilanci da bangaranci su hada kawunansu don hakan ne kawai zai kawo canji.
Your browser doesn’t support HTML5