Kauda Kai Na Ruruta Wutar Rikici-Paparoma Francis

Pope Francis

Paparoma Francis ya kushewa kauda kai da ake yi da ya ruruta wutar tashe tashen hankali dake janyo asarar rayuka da kuma tilasawa al'umma kauracewa kasashensu.

Paparoma Francis ya yi Allah wadai da nuna halin ko in kula da ya sa tashin hankali ya mamaye gabas ta Tsakiya ya kuma yi sanadin raba dubban mabiya addinin kirista da muhallansu.

Paparoman yana jawabi ne yau asabar da safe a birnin Bari na kasar Italiya a wani taron addu’oi na shugabannin darikar Katolika, na neman zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Paparoma Francis yace, kamar haske a cikin duhu, Kiristoci da suke fuskantar kuntatawa a gabas ta tsakiya suna ci gaba cikin bangaskiyarsu duk da matsi da suke fuskanta.

A cikin addu’arshi ta farko, Paparoma Francis yace Gabas ta Tsakiya ita ce tushen addinin Kirista, inda al’adun kirista da asalinsu suke.

Paparoma Francis ya dade yana bayyana damuwa game da yadda ake korar mabiya addinin kirista daga muhallansu a gabas ta tsakiya. Adadin kirista a yankin ya ragu matuka a cikin shekarunnan, sabili da kuntatawa kiristoci da masu tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama ke yi, da yake-yake, da kuma rashin tabbas a fannin harkokin siyasa da tattalin arziki.

Duk da haka Paparoman yace, yankin dake cike da haske a shekarun baya, yanzu ya bakanta, da gajimaren yaki da tashin hankali, da lalata kaddarori da mamaya wadansu lokuta da masu tsattsauran ra’ayin addini ke yi, da kauracewar al’umma ala tilas, da kuma kyaliya.

Paparoman ya kara da cewa, dukan wadannan suna faruwa yayinda da dama ke nuna halin ko in kula, Yace Gabas ta Tsakiya ta zama kasar da al’ummarta ke ficewa daga kasarsu.