Bayan da yan bindiga dadi da masu satar mutane suka dai-dai ta da dama daga cikin yankunan jihar Zamfara, wannan ta’addancin dai halin yanzu na neman samun gindin zama a jihar Katsina.
A cikin kanan hukumoni tara dake dandana kudarsu, karamar hukumar Batsari itace kan gaba inda yau kwanaki shidda ke nan jere 'yan bingigan suke tada gari.
Malam Sani Lawal wani mazaunin Karamar hukumar da Muryar Amurka ta yi hira da shi ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun kai hare hare a kauyuka da dama inda suka yi kone kone suka kuma janyo asarar rayuka da kaddarori. yace sun je Kasai da Wagini suka kashe mutune sannan suka kore masu dabbobi. Bisa ga cewarshi, 'yan bindigar sun kuma tafi garin Yar’gamji suka kashe mutane goma sha ukku, wadanda aka kai gawarwakinsu kofar gidan sarkin Batsari.
Mallam Lawal ya bayyana cewa, wadansu mutanen an kashe su ne suna gonakinsu, yayinda yace 'yan bindigar sun tada mutanen karamar hukumar Safana baki daya, sai dai Sashen Hausa bai sami tabbacin haka daga wata majiya ba. Mallam Sani Lawal dai ya bayyana fusata da bakin cikin ganin a cewarsa, gwamnati bata daukar matakin da ya kamata na shawo kan matsalar.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5