Yanzu haka al'ummomi a wasu jihohin arewacin Najeriya na cikin yanayin dokokin da gwamnatocin su suka dauka don kawo karshen ‘yan fashin daji koda za a samu sauki ga matsalolin da suke haifarwa, ciki har da katse hanyoyin sadarwa.
Wannan yanayin dai bai hana ‘yan fashin dajin ci gaba da kai farmaki ga jama'a ba duk da yake wadannan dokokin suna shafar su.
A jihar Sokoto dake arewa Maso yammacin Najeriya, irin haka na ta faruwa kamar yadda barayin suka shiga yankin Gudu dake arewacin jihar suka sace wata matar aure, su kuwa ‘yan banga suka bi sawunsu cikin daji inda har aka zubar da jini.
A yankin Goronyo ma bayanai sun nuna ‘yan bindigar sun shiga yankin suna harbin kan mai uwa da wabi, inda suka hallaka mutane akalla hudu.
Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka ya nemi jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya ta bakin kakakin ta a Sokoto ASP Sanusi Abubakar, amma dai ya ce babu wani bayani a hukumance.
‘Yan Najeriya na ci gaba da mamakin daukar matakan da ake yi amma kuma ba a yi wata azama ba ta farautar barayin, domin matakan kadai ba zasu kawo sauki da kan su ba dole sai an motsa, a cewar Bashir Altine Guyawa shugaban rundunar adalci a jihar Sokoto.
A jihar Kebbi ma yankin Bena dake masarautar Zuru, matakan da aka dauka suna ci gaba da ta'azzarar da lamurran rayuwa acewar wasu mazauna yankin.
Dama dai masu sharhi akan lamurran yau da kullum musamman akan harkar sun bayar da shawarar cewa kamata yi wadannan matakan da ake dauka su kasance na wani Dan lokaci domin idan suka tsawaita sukan iya haifar da wasu matsaloli na daban.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5