Samira Kassim ta kasance mace mai karatu a fannin kasuwanci a School of Management Studies da ke Kano a Nijeriya, a cewarta, domin ta inganta harkokin sana’arta da zarar ta kammala karatun ta na gaba da sakandare, ko da ba ta yi aikin gwamnatin, ko na kamfanoni masu zaman kansu ba, za ta iya sarrafa aiki da karatunta a zamanance.
A yanzu mafi yawan maza ba sa barin matansu su fita aiki, da zarar mace ta yi karatun boko zai ba ta damar sarrafa karamar sana’ar, zuwa babban aiki da zai kawo mata ci gaba sannan kuma a zamanance, da kuma iya daukar wasu aiki.
Ta kara da cewa tana karatu ne ko ba komai za ta yi aikinta a cikin gida, sannan abubuwa da dama ne suka ja ra’ayinta ta fara karatu, ganin cewar mafi yawan mata ba sa son fita aiki a mafi yawan lokutan ko da kuwa sun fita sukan fuskanci matsalolin na tauye musu hakki.
Samira ba ta sha'awarar aikin gwamnatin ko na kamfani domin aiki a karkashin wani yana tauye hazakar mutum, sannan ilimi a yanzu shi ne abu da ya dace a kowace mace na dashi, idan kuma aka ce mace ba ta da ilimi to ba za ta yi daraja ba a gaban mijinta ma.