Shirin kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya leka kasuwar Mu da Lawal da ke garin Bauchi, bangaren ‘yan panteka don jin yadda harkokin kasuwar ke tafiya.
BAUCHI, NIGERIA - Harkar kasuwancin panteka abu ne da ya kunshi saye da sayar da kayayyaki iri dabam daban, da suka hada kayayyakin aikin gini, injina da sauran karahuna.
Wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad, ya ziyarci kasuwar da ake hada hadar panteka, inda ya tattauna da masu sana’ar, da masu sayen kayayyaki, da ma matasan da suke koyon sana’ar panteka.
Saurari cikakken shirin cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5