Kashi Arba'in Cikin Dari Na Yaran Afghanistan Basu Zuwa Makaranta

Wadansu yara suna wasa a inda ake makaranta

Wani sabon rahoton da aka buga a kan harkokin ilimi a Afghanistan ya bayyana cewa, kimanin kashi arba’in da hudu cikin dari na dukan kananan yaran dake kasar basu zuwa makaranta, abinda ya kara yawan adadin karon farko tun shekara ta dubu da dari biyu da biyu.

Rahoton ya dora alhakin kan rikicin da kuma matsalar rashin tsaro dake kara tsananta da ya hada da talauci da yayi Kamari, da kuma wariya da ake nunawa ‘ya’ya mata, da ya shafi kananan yara miliyan uku da dubu dari bakwai dake tsakanin shekaru bakwai zuwa goma sha bakwai da basu zuwa makaranta.

Ministan harkokin ilimi na kasar Afghanistan Mirwais Balkhi ya tattauna a wajen wani taron bita a Kabul yau Lahadi, rahoton da asusun UNICEF da kuma cibiyar tallafawa bunkasa ayyukan kasa da kasa da kuma Samuel Hall wani kwararre mai zamana kansa suka wallafa.

Ya bayyana cewa, yara mata ne kashi sittin cikin dari na adadin yaran da basu zuwa makaranta.

Rahoton ya gano cewa, kashi tamanin da biyar cikin dari na 'yammata basu zuwa makaranta a lardunan da lamarin yafi muni da suka hada da Kandahar, Helmand, Wardak, Paktika, Zabul da kuma Uruzgan.

Biga ga rahoton kuma, aurar da yara da wuri, da kuma kaurar da jama'a ke yia Afghanistan sakamakon tashin hankali yana shafar zuwa makarantar yara..

Banda haka kuma, akwai karancin malaman makaranta mata, da rashin kayan ilimantarwa masu inganci, da matsalar tasro da yake hana ayyukan makaranta a yankunan da ake tashin hankali yana hana yara musamman mata zuwa makaranta.