Kasashen nahiyar turai sun yi ca akan hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA kan kin sallamar Rasha a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
A ranar Alhamis Rasha ta kai mamaya kasar Ukraine, lamarin da ya haifar da mummunar suka daga mafiya kasashen duniya.
Kasar Poland wacce za ta kara da Rashar a ranar 24 ga watan Maris a wasannin shiga gasar wacce za a yi a Qatar a bana ta janye daga wasan.
Bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, FIFA ta haramta wa Rasha amfani da tutarta da rera taken kasar tare da kuma yin wasa karkashin sunan "Football Union of Russia."
“A yau, ba za mu lamunci matakin da FIFA ta dauka ba (kan Rasha)” Shugabar hukumar kwallon kafar kasar Poland, Cezary Kulesza ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Poland ta kara da cewa, “ba mu da sha’awar yin wannan wasa. Matsayarmu a bayyane take: Tawagar ‘yan wasan Poland ba za ta wasa da Rasha ba, ko da wane irin suna tawagar ‘yan wasan ta zo da shi.”
- Wannan labarin na kamfanin dillancin labarai na AP ne wanda Mahmud Lalo ya fassara.