Kasashen Nahiyar Asiya Da Turai Zasu Tallafawa Rundunar Tsaro Ta G5

Shugaban kasashen yankin Sahel tare da Shugaba Emmanuel Macron a ganawarsu jiya.

Taron shugabannin kasashen yankin Sahel, da na wasu kasashen Turai da kuma Asiya da ya gudana jiya Laraba a Faransa ya bada sanarwar samarda miliyan fiye da 100 na dalar Amurka a matsayin gudunmuwa don gudanar da ayyukan rundunar hadin guiwar G5 Sahel mai yaki da ta’addanci a yankin na Sahel.

Tallafin wanda a jimilce ya tashi Euro 135, ya fito ne daga kasashen Saudiyya mai miliyan dari, yayin da Daular larabawa ta kudiri aniyar bayarda miliyan talatin, sai kasar Holland da ta sanar da zuba miliyan biyar, wadanda za a yi amfani da su domin cigaban ayyukan rundunar hadin guywar G5 Sahel dake fama da rashin kudaden gudanar a yakin da ta kaddamar akan ‘yan ta’adda a yankin kasashen Sahel.

Dakta Sani Yahya Janjuna, mai sharhi akan al’amuran tsaro ya fadi cewa kudi da makamai na da muhimmanci a yaki amma zuciya ce ke yin yaki. Sai dai ya ce matsalar yaki shine ba a san lokacin da za a gama shi ba. Ya cigaba da cewa, tayiwu wannan gudunmuwar tallafin ta isa a halin yanzu amma kuma idan yakin ya jima, to dole a kara neman taimako daga wasu kasashen.

Tun a ranar farko da aka kafa rundunar, kasashen dake da hannu wajen tafiyar da ita, da suka hada da Nijar, Mali, Burkina Faso, Mauritania, da Chadi, sun dauki alkawarin bada miliyan goma na Euro

Sai dai a yayinda wasu ‘yan Nijar ke yabawa da wannan yunkuri wasu kuma na cewa koma baya ne ga kasashen Afrika.

Jami’in fafutika Abdu Idi, ya ce bai gamsu ba, saboda ba kodayaushe ne kasashen Turai ke cika alkawarin da suke dauka ba, kamata yayi ace kowacce kasa cikin kasashen biyar ta fito da miliyan dari ba sai anje neman taimako ba.

Daga cikin miliyan dari hudu da hamsin da ake bukata, tuni Amurka ta bada tallafin miliyan sittin na dala yayinda kungiyar Tarayyar Turai ta bada miliyan hamsin na Euro, ita kuma kasar Faransa ta bada tallafin kayan yaki da aka kiyasta darajarsu zata kai miliyan goma na Euro.

Kasar Nijar dake kan gaban wadanda ke fatan ganin an murkushe ayyukan ta’addanci a baki dayan yanki Afrika ta yamma, a taron na jiya Laraba ta bayyana shirin kara yawan dakarunta a rundunar hadin guywar, matakin da wasu ke dauka tamkar amsa ga kasashen da har yanzu suke dari-darin aika askarawansu cikin wannan rundunar wadda tun tashin farko take bukatar sojoji dubu biyar.

Ga karin bayani daga wakilin sashen hausa Sule Mumuni Barma cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Kasashen Nahiyar Asiya Da Turai Zasu Ba Rundunar Hadin Guywar G5 Sahel Tallafi - 2'53"