A wajen bikin bude dakin taron kasa da kasa na Mahatma Gandhi International Conference Center da aka yi a Nijer, Shugaba Issouhou Mahamadou, wanda ya jagoranci taron ya bayyana ginin a matsayin wani abu da daukacin ‘yan Nijar za su yi alfahari da shi saboda yadda zai karawa kasar daraja da kima a idon duniya.
Jamhuriyar Nijar da kasar Indiya sun kudiri aniyar fadada huldar da ke tsakaninsu zuwa fannonin tsaro, da kiwon lafiya bayan da gwamnatin Firai Minista Narendra Modi ta ginawa Nijar wani dakin taro kyauta, wanda aka kiyasta darajarsa ta kai biliyan talatin na CFA, a matsayin wani bangare na alkawuran da kasar Indiya ta dauka a karkashin yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma.
Hulda tsakanin kasar Indiya da kasashen Afirka wani abu ne mai dadadden tarihi, wanda akan gani ta hanyar al’adu da yanayi da muhallin yankunan biyu inji Ministan Harakokin Wajen kasar Indiya, Dr. S. Jaishankar, a lokacin da yake jawabi a yayin mikawa hukumomin Nijar makullan dakin taron na Mahatma Gandhi mai kujeru dubu biyu da dari da sha biyu wanda kasar Indiya ta gina kyauta a birnin Yamai.
Ayyukan samar da makamashi da kuma noma, da kiwo su ne fannonin da kasashen biyu suka fi baiwa fifiko a shekarun baya, to amma lura da kyakkyawan sakamakon da wannan hulda ta bayar ya sa kasashen biyu yanke shawarar fadada huldar zuwa fannin tsaro da kiwon lafiya, inji Ministan Harakokin Wajen Nijar Kalla Hankourao.
A karkashin yarjejeniyar kasashen biyu, Nijar ta sakarwa kasar Indiya ragama domin sayen amfanin gona da na kiwon da Allah ya horewa talakawan kasar.
A saurari rahoto cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5