Hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wasu biranen kasar Saudiya da suka hallaka mutane hudu tare da jikata wasu biyar a Medina sun harzuka wasu kasashen duniya wadanda suka yi allawadai da hare-haren da babban lafazi..
Amurka tayi tur da hare-haren da aka kai ranar Talata kan Saudiya. Shekaranjiya ta yiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta'aziya tare da jaddadawa wadanda suka jikata a biranen Jeddah da Qatif da Medina a wata sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar.
Sanarwar tace "wadannan hare-haren sun kara nanata irin kalubalen da dukanmu muke fuskanta kuma tuni ne cewa akwai bukatar mu cigaba da yin takatsantsan wajen yaki da masu ra'ayin rikau domin a zakulosu su fuskanci shari'a", inji sanarwar.
Sanarwar ta cigaba da cewa Amurka tana tare da al'ummar Saudiya yayinda suke fuskantar wannan kalubale.
Kasar Rasha ma ta fitar da sanarwar da tayi allawadai da hare-haren wadanda ta kira muggayen laifi da 'yan ta'ada suka aikata kuma ta sake jaddada matsayinta cewa a yaki wannan bala'i ba sani ba sabo. Ta kira kasashen duniya su hada kai ba tare da wani banbanci ba su kawar da wannan shaidancin.