Shugabannin yankin Catalonia na fuskantar karin matsin lamba daga gida da kasashen waje kan cewa su watsar da shirinsu na ayyana cin gashin kai daga Spain, gabannin jawabin shugaban yankin da aka shirya yi.
A yau Talata ne aka shirya shugaban yankin Carles Puigdemont, zai yi jawabi gaban ‘yan majalisar dokokin yankin nasa, hakan yasa gwamnatin Spain ta shiga damuwa da tsoron kada ‘yan majalisar su kada kuri’ar yarda da yunkurin neman yancin kan.
A kan hakan ne, shugabannin siyasa na ciki da wajen kasar jiya Litinin suke kira ga shugabannin Catalan da su dakatar da shirinsu don samar da zaman lafiya a kasa baki daya.
Magajiyar Garin birnin Barcelona itace wadda tayi magana a baya-bayannan inda ta nuna rashin goyon bayanta da rabuwar kasar, tana mai cewa hakan zai iya saka al’umma cikin wani hali. Ada Colau, tayi kira ga duk bangarorin da wannan lamari ya shafa da su zauna don samo hanyar warware matsalar da ba taba ganin irinta a tarihin dimokaradiyyar Spain ba.