Taron ya samu halartar kasashe irinsu Chadi, Tunisiya, Mauritania, Algeriya, Sudan, Nijar da wakilan Tarayyar Afirka da na Turai da wakilin Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Libiyan.
Taron ya zo ne a daidai lokacin da shirin zaman lafiyar kasar ta Libiya yake tanga-tanga sakamakon rashin jittuwa tsakanin 'yan kasar tun lokacin da aka hambarar da gwamnatin Muammar Ghadafi.
Ministan harkokin wajen kasar Nijar Ibrahim Yakuba shi ya yiwa 'yan jarida karin bayani akan taron. Yace sun bada shawarar a kafa gwamnatin da kowa ya yadda da ita. Yace yanzu kasar bata zaunuwa saboda ba'a nemi shawarar wasu ba.
Malam Ibrahim Yakuba yace kafin a samu gwamnatin da kowa zai amince da ita sai an kafa rundunar sojojin kasar, mai shugabanci guda da kowa ya amince da ita. Libiya tana da tarihi saboda haka kowa sai an sashi cikin samarda rundunar soji ta bai daya da kuma gwamnati karbabbuwa. Duk wadanda turawa basa son a sa cikin shawara kamar bangaren Ghadafi dole ne a sasu.
Shawara ta ukku ita ce yin yaki da ta'adanci gadan gadan. Akwai 'yan Boko Haram a Libiya tare da duk wata kungiyar ta'adanci suna kasar. Ba zata yiwu a kafa gwamnati a kasar ba sai an yaki 'yan ta'ada.
Taron na ministocin harkokin wajen kasashen ya bullo da wasu sabbin shawarwari bayan yin la'akari da cewa kasashen sun fi kowace kasa dandana kudar irin abubuwan dake faruwa a kasar Libiya.
A cewar Ibrahim Yakuba kodayaushe kasashen turawa suka shiga cikin rikicin wata kasa ba sa aikata alheri. Yayi misali da Somalia,da Iraqi da Libiya. Yace babu kasa guda inda suka ci nasara. Rikicin Libiya na 'yan kasar ne tare da kasashen dake makwaftaka da ita. Saboda haka a bar mata ta warware matsalarta. Idan Libiya ta lalace kasashen dake makwaftaka da ita tasu ma ta lalace.
Shi ma wakilin Majalisar Dinkin Duniya dake Libiya yace yin anfani da karfin soja ba zai warware rikicin kasar ba saboda haka dole ne a bi hanyar tuntuba tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna domin cimma daidaito da zai bada damar kafa gwamnatin hadin kan kasa. .
Wani kalubale dake fuskantar kasashen dake makwaftaka da Libiyan shi ne matsa kaimi ga ayyukan tsaro kan iyakokinsu da kasar saboda makamai fiye da miliyan 26 ne ke yawo cikinta.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5