Ministocin kungiyar kasashen CONSEIL DE L'ENTENTE da suka hada da Nijer,Cote d'ivoire,Burkina fasso,Benin,da Togo na halarta wani taron kolin kasashen domin duba matsalolin da kasashen minbobin kungiyar ke fuskanta.
Taron na wuni daya da ministocin kasashen Conseil De’ L’entente ke halarta a birnin Niamey zai tattauna ne a kan matsolin da kasashe biyar membobin kungiyar ke fuskanta da suka hada da matsalolin tsaro da kiwon lafiya da bunkasar tattalin arziki.
Taron zai kuma tattauna a kan sauran matsaloli da kasahen kungiyar ke fuskanta.
Taron dai yazo ne a daidai lokacin da kasashen ke fuskantar wadansu matsalolin tsaro da suka shafi ayyukan ta’addanci.
Daga Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko mana da wannan rahoton
Your browser doesn’t support HTML5