Manyan kasashe biyar da karfin tattalin arzikinsu ke habaka a duniya sun kara jaddada tsarin harkokin cinikayyar da ake tsakaninsu.
Kasashe sun kuma sha alwashin kara karfafa hadin kansu ta fuskar tattalin arziki.
Wannan matsaya ta su na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke barazanar sanya kudaden haraji da kuma yadda take gaban kanta kan harkokin kasuwancin duniya.
Kasashen wadanda aka fi saninsu da BRICS a takaice, sun hada da Brazil, Rasha, India, China da kuma Afirka ta Kudu.
Sun hadu ne a birnin Johannesburg a taron kolin da suke yi na shekara-shekara, inda hankulan mahalarta taron suka karkata kan barazanar da ke tattare da takaddamar cinikayya da Amurka take azazzalawa.
Ko da yake, ba su fito fili sun kama sunan shugaba Donald Trump ba.
“Muna cikin damuwa kan yadda tasirin manufofin tattalin arzikin wasu manyan kasashen suke yaduwa.” Inji wata sanarwa ta hadin gwiwa da kasashen na BRICS suka fitar.