A yayinda aka fara wani taron samun zaman lafiya a kasar Uganda, shugabannin kasashen gabashin Africa sun bayyana cewa suna bukatar samar da wata sabuwar hanyar samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a kasashen su a yunkurin su na ganin sun yaki ayyukan assha, Rashin zaman lafiya da da talauci.
Jakada Fred Ngoga Gateretse wanda ke jagorantar sashen dakile rikici da gabatar da kashedi na kwamitin kungiyar hada kan kasashen Afrika, yace ya lura kungiyoyin ‘yan tadda irin su Alshabab na kasar Somalia har sun fi wasu gwamnatocin Africa tsari.
Yace kasashen na Africa basu da hadin kai. shin ko kun san ko wane irin tsawon lokaci yake dauka domin samar da ‘yan kunar bakin wake, wannan yakan dauki a kalla watanni 6 zuwa 7, haka kuma, kun san tsawon lokacin da yake dauka domin samar da maaikacin gwamnati a MDD ko kuma kungiyar tarayyar Africa, yana daukan kusan watanni 19, don haka me wannan yake nuna maka, wannan yana nufin masu aikata ayyukan assha sunfi tsari fiye da mu’’
Wadannan sune kalaman jakada Gateretse.