Kasashe Sun Fara Binciken Faduwar Jirgin Ukraine a Iran

Iran

Kasar Iran ta gayyaci hukumar kula da harkokin sufuri, da hukumar binciken hadurra ta Amurka, NTSB a takaice, don su shiga binciken da ake yi game da faduwar jirgin saman fasinjan Ukraine a kusa daTehran, babban birnin Iran a cikin farkon makon nan.

A wata sanarwa da aka fitar jiya Alhamis, hukumar ta NTSB ta ce ta sami sakon gayyata a hukumance game da faduwar jirgin saman daga hukumar sa ido akan hadurran jiragen saman Iran kuma za ta tura wakilinta don gudanar da bincike akan hadarin.

Haka kuma Iran ta gayyaci kamfanin Boeing, kamfanin Amurka dake kera jirgin saman, don a yi bincike da shi. Ita ma Ukraine ba za a bar ta a baya ba, za ta shiga tawagar masu binciken.

A Amurka kuma Majalisar Wakilai mai rinjayen ‘yan jam’iyyar Democrat ta kada kuri’a jiya Alhamis kan takaita ikon Shugaba Donald Trump na neman kara kai hare-hare akan Iran ba tare da amincewar Majalisar Dokokin kasar ba.

Kudurin ya sami amincewa da kuri’u 224 akasain 194. Wasu ‘yan Republican su uku suma sun jefa kuri’ar amincewa da kudurin kamar ‘yan Democrat.

Ana ganin a mako mai zuwa ‘yan Majalisar Dattawan kasar su kuma za su kada kuri’a kan wani kuduri mai kama da wannan

‘Yan majalisar wakilan sun gabatar da wannan kudurin ne bayan da Trump ya bada umurnin kai wani hari da jirgi mara matuki a makon da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar Janar Qassem Soleimani, kwamandan rundunar sojan juyin juya halin Iran.