Kasashe Na Kara Daukar Matakan Takaita Tafiye-tafiye Sakamakon COVID-19

Kasashen Jamus da Faransa zasu sanya sabbin matakan takaita tafiye-tafiye saboda annobar COVID-19.

Yayin da adadin masu kamuwa da cutar coronavirus ke ci gaba da karuwa kuma wasu sabbin nau’ikan cutar suka bullo, wasu kasashe na sanya sabbin matakan takaita tafiye-tafiye.

Kasar Faransa ta hana tafiye-tafiye daga duk kasashen da ba sa karkashin tarayyar Turai. Bisa ga sabon matakin wanda zai fara aiki ranar Lahadi 31 ga watan Janairu, matafiya daga kasashen tarayyar Turai da ke son shiga Faransa dole ne su nuna shaidar takardar gwaji da ta nuna ba sa dauke da cutar coronavirus.

Matafiya daga kasashen Turai da na Afrika da yawa, kamar Brazil, Birtaniya, Eswatini, Ireland, Lesotho, Portugal da Afrika ta kudu, ba za a a barsu su shiga Jamus ba. Ko da ya ke, matafiya da ke zama Jamus da suka fito daga wadannan kasashen za a bari su shiga kasar ko da suna dauke da cutar ta coronavirus.

An killace wasu daliban jami’ar Michigan da ke Amurka su 14 bayan da aka gano suna dauke da sabon nau’in coronavirus na kasar Birtaniya. An sami rahoton cewa daya daga cikin daliban ya je Birtaniya a lokacin hutun hunturu.